Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na bakwai

Mene ne hukuncin iddar macen da ba ta yin haila ko kuma tana yi sai wata biyu ko uku?
TAMBAYA: Akramakallahu. Ko mutum zai iya yin salla a cikin mota don tsoron fitar lokaci?
Daga Lawali Sulaiman Maikwalli Uban Doma Road Kofar Atiku, Sakkwato
SHAIKH ZAKZAKY: To sai dai a surar cewa ana tafiya da shi bisa dole ne. Kuma ko wannan ma zai zama 'ada'i' ya fadi a kansa. Amma in ba haka ba, in shi ke tuka motar ko kuma shi fasinja ne yana da ikon ya ce a dakata, to lallai lazim ne ya tsaya ya sauka kasa ya yi salla din. Wato muna iya cewa ma ba zai yiwu ba. Idan kuma a surar tilas aka yi masa, kamar a ce an kama shi ne aka tilasta masa aka yi ta jan shi a mota, to "ada'i" ya fadi a kansa saboda rashin zuhuraini. Saboda haka sai ya bari in ya sauka kasa ya biya. Sawa'un ko da lokacinta ya fita. Amma zai iya yin sallar dare na nafila, misali a cikin mota, wannan kuma ko da ba yana kallon alkibla bane. Amma hukuncin mota a nan ya bambanta da na jirgin ruwa ko jirgin sama ko na kasa, wanda su wadannan zai iya yin sallah mai ma'abociyar sujada da ruku'u a cikinsu, wato mota a nan ta zama tamkar doki kenan wanda shi ba zai yiwu ya yi irin wadannan ba. Saboda haka wajibinsa shi ne ya sauko.
TAMBAYA: Na yi alkawarin zan yi azumi bakwai idan wani mara lafiya da nake da shi a asibiti ya warke, to sai ya sami sauki, amma bai warke ba, bayan kwana kadan sai rashin lafiyar ya sake dawowa har na kashe kudi sosai, sannan ya warke. Shin wannan azumin na nan ko ya fadi?
SHAIKH ZAKZAKY: Lallai tun da dai ka ce in ya warke ne, to ai ya warke din, komin dadewa in dai har ya warke, shi kenan yanzun dole ka cika wannan alkawarin. Kuma da zaran ya warken ne za ka cika wannan alkawarin. Saboda haka yanzun ma har ka yi wani laifi na jinkirta cika wannan alkawarin.
TAMBAYA: Akramakallahu. Mutum ne yake da kaya masu najasa sai ya wanke su da omo ko da sabulu.Shin ya wadatar?
SHAIKH ZAKZAKY: To na san wadannan abubuwan lallai ba za su iya wankewa ba tare da ruwa ba. Saboda ko da omon na ruwa ne ya dunga zuba ma shi, ba zai yiwu ya wanke ba, haka kuma sabulun ko da na ruwa ne ba zai wanke ba. Saboda haka abin sani dai shi ne, dole ita najasa ana wanke ta ne da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa. Saboda haka ko ya sa sabulu dole ya zama karshe dai ruwa wanda yake 'mudlaki' kuma mai tsarki, shi ne ya wanke mahallin najasa din ya fid da shi.
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ko ya halasta Nurse namiji ya karbi haihuwa, idan asibitin da yake mata sun yi karanci kuma ta nemi taimako?
Daga Buhari Musa Tofa, Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To dole ya kiyaye, ya tsaya a kan abin da ya zama dole. Alal misali in zai iya da taimakon yin bayani gare ta ta taimaki kanta ba tare da ya kai hannunsa ko ya kalle ta ba, sai ya yi haka nan. In kuma ya zama dole taimakon ba zai iya ganewa ba sai ya duba wani abu, kamar zai zama sai ya duba ta madubi sai ya zama sai ya duba ta madobin. Wato ba zai yiwu har ya je ya duba ya kai hannunsa ba, har sai inda ta kai fuskar cewa za ta iya mutuwa ko jaririn ya rasu. Wato kuma ba zai halatta masa ba ya yi matakin da zai yiwu ya yi kasa da shi ba.
TAMBAYA: Akramakallahu. Menene hukuncin iddar macen da ba ta yin haila ko kuma tana yi sai wata biyu ko uku?
Daga Buhari Musa Tofa, Kano
SHAIKH ZAKZAKY: To in ba ta haila samsam ne, ya danganta da irin idda din da kuma lokacin da ya auku. Kamar idan iddar wafati ne, bai shafi hailarta ba. Idan iddar saki ne, sakin kuma an sake ta a bayan an tabe ta, to sai ta yi da watanni uku kenan. Idan kuma sakin da ba a tabe ta bane, to ba ma idda a kanta samsam. Idan kuwa tana yi wata bibbiyu ne, to lallai "Salasatu kuru'i" din za ta yi. Matukar tsakanin wani haila da wani haila bai kai wata uku cur ba. In tana tsarkin wata bibbiyu ne, to lallai tsarki uku din za ta yi. Sai dai in tsarki ya kai wata uku, to shike nan ya fid da ita haila. Idan aka sami wata uku cur ba ta yi haila ba, shi kenan iddarta ya kare.
TAMBAYA: Akramakallahu. Menene hukuncin wanda ya yi harama da hajji sai wani abu ya yanka masa hannu, amma jini bai fito ba?
SHAIKH ZAKZAKY: To ai ya ce wani abu ne, ba shi ya yanka ba. Ai an hana mutum shi ya cizge fatar jikinsa ne, ba a ce in wani abu ya cizge masa, ba shi ne ya cizge da kansa ba, sai ya zama laifi ba. Idan wani abu ne ya same shi ba shi ya sama wa kansa ba, ba laifi a kansa. Sai da in shi ne ya yi sake har ta kai ma fata ta daye. Kuma ko da jini bai fita ba, in ya kwantala fata, amma jini bai fito ba duk ya aikata haram, wanda yake kuma akwai fidiya. Amma banda abin da ya same shi, ba shi ya yi sanadi ba.
TAMBAYA: Akramakallahu. Ko zai inganta mabiyin mazhabar Ahlul Baiti ya yi aikin hajji bisa jagorancin mabiyin wata mazhabar ta daban?
SHAIKH ZAKZAKY: To, ba mu san cewa shi Hajji ana yi da wani jagoranci ba. Abin da aka sani dai shi ne, shi aikin hajji akwai abubuwan da yake lazim ne mutum ya yi. Akwai rukunnai, akwai wajibai, akwai mustahabbai, akwai haramun, akwai halas. To sai ya yi Hajjin kamar yadda koyarwar mazhabarsa ta nuna. Amma lallai ba a wani jagora a Hajji. In yana nufin dan jagora wanda zai nuna masa wurare ne, to ai ba shi ne yake masa aikin ba, shi aikinsa daban, ba kamar salla ne da ake bin Liman ba. Kuma ko sallar ne ma ai an yarda ana bin Liman. Ballantana shi wannan aikin da aka sa masa daban ne, ko da kun yi Hajji tare da wani.
YAMBAYA: Akramakallahu. Mutum yana iya amfani da mahangayya na zamani kamar "scanning"wajen tantance tsarkin mace ko cikinta ba sai ta yi jini ba don sakinta?
Daga Aliyu Musa Ali Unguwar Dosa Kaduna
SHAIKH ZAKZAKY: Ma'aunan dai da shari'a ta sa, dole da shi ne za a yi amfani. Saboda haka idan da wata ala ta zamani da za su nuna wani abu, in wannan alar za ta nuna wani abu amma ma'aunin shari'a ba zai nuna ba, wanda aka sani, kamar shigar da auduga da fitar da shi, to da na shigar da auduga da fitar da shi din za a yi amfani. Sai dai ba mu ce wannan ba zai iya taimakawa ba, amma ba zai zama shi ne mai hukuncin karshe ba.
TAMBAYA: Akramakallahu. Auren mutu'a yana halatta wa mijin da ya saki matarsa saki uku ya dawo da ita ba tare da ta yi aure da'imi ba?
Daga Baba Sani Limanci Kano
SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani shi ne aure sahihi da taki sahihi, shi ke halatta mace ga wanda ya sake ta saki uku a lokuta daban-daban, don ya warware igiyar auren farko din. Aure sahihi, ya take ta kuma taki sahihi. Sannan suka rabu ta yi idda ta kare, sannan take iya halatta ma wanda ya sake ta uku a baya.
TAMBAYA: Akramakallahu. Yaya mutumin da yake tafiya a jirgin sama zai yi idan lokacin salla ya yi?
Daga Baba Sani Limanci Kano
SHAIKH ZAKKZAKY: To idan yana sa rai jirgin zai sauka kasa kafin lokacin sallar ya wuce kuma har ya samu ya yi sallar a kasa, to ya samu ya yi jinkiri har ya zuwa wannan lokacin. Amma in yana jin tsoron ficewar lokaci, tun farkon lokacin ma in ya so yana iya yin sallarsa. Saboda a sama akwai ruwa da kasa. Amma sai dai bai yi daidai da kamar kasa din ba wajen samun natsuwa.
.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved